Wasu Sojojin Libiya Sun Rasa Ransu A Gumurzu Da Mayakan Kungiyar Da'ish
Dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnatin Libiya da mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish ya lashe rayukan sojoji akalla bakwai tare da jikkatan wasu fiye da ashirin da biyar a kusa da garin Sirt.
Sojojin Libiya karkashin gwamnatin rikon kwarya sun yi dauki ba dadi da wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Da'ish a kusa da garin Sirt a jiya Juma'a lamarin da ya janyo hasarar rayuka a tsakanin bangarorin biyu, inda wata majiyar rundunar sojin kasar ta ce yawan sojojin da suka rasa rayukansu sun kai bakwai tare da jikkatan wasu akalla ashirin da biyar na daban.
Har ila yau sojojin gwamnatin na Libiya sun fafata da mayakan kungiyar ta Da'ish a kudu maso gabashin garin Abu-Qarin da kuma gabashin garin Misrata, inda sojojin na Libiya suka yi nasarar halaka mayakan kungiyar ta Da'ish da dama tare da kwasar ganimar makamai.