An tsarkake wani yanki na arewacin kasar Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5905-an_tsarkake_wani_yanki_na_arewacin_kasar_libiya
Dakarun tsaron Libiya dake kalkashin Gwamnatin hadin kan kasar sun tsarkake wani yanki na garin Syrte daga 'yan ta'addar ISIS
(last modified 2018-08-22T06:58:21+00:00 )
May 28, 2016 06:41 UTC
  • An tsarkake wani yanki na arewacin kasar Libiya

Dakarun tsaron Libiya dake kalkashin Gwamnatin hadin kan kasar sun tsarkake wani yanki na garin Syrte daga 'yan ta'addar ISIS

Rundunar tsaro mai lakabin Bunyanul-marsus dake kalkashin ikon sabuwar Gwamnatin hadin kan kasa ta kasar Libiya ta sanar a yau cewa bayan wani gumurzu mai tsanani tsakaninsu da mayakan 'yan ta'addar ISIS sun samu nasarar tsarkaka yankin Bawabatu Salasin na yammacin garin Syrte daga hanun 'yan ta'addar ISIS.

Rundunar ta ce ta hallaka tare da jikkata mayakan ISIS da dama, inda ita kuma a nata bangare ta yi hasarar sojoji guda biyu.

Rahoton ya ce bayan kashi da kungiyar ISIS ta ta sha a Bawabatu Salasin ta bar gawawwakin mayakan ta kimanin 35 a gurin.

Har ila yau Rahoton ya kara da cewa Dakarun tsaron Libiyan na ci gaba da kutsawa yankunan dake gefen garin Syrte wanda shine babbar tungar 'yan ta'addar ISIS din a kasar ta Libiya.