Libya : Dakarun Gwamnatin Hadaka Sun Kwace Gariruwa 2 Daga Hanun (IS)
Dakarun gwamnatin hadaka a Libya sun sanar a wannan Talata da kwace ikon gaririwan Ben Jawad da kuma Nofliya dake gabashin Syrte daga hannun 'yan ta'adan ISIS.
Hakan dai a cewar wata sanarwa daga ma'aikatar tsaron ta GNA, ya biyo bayan kutse da dakarun sukayi a wannan Talata a Syrte inda kuma sunyi nasara kwace daukacin ikon gaririwan biyu.
Dama kafin hakan wata arangama da akayi a wannan Litinin tsakanin rundinar tsaro cibiyoyin adanon man fetur da 'yan ta'adan na ISIS tayi sanadin mutuwar mutane biyar tareda jikkata wasu 18, kamar yadda kwamadan rundinar yankin da lamarin ya auku, kanal Bashir Bouthefira ya tabbatarwa da kanfanin dilancin labaren faransa na AFP.
Kawo yanzu dai a cewar kanal Bouthefira dakarun kasar sun dushi yankin Harawa shi ma dake gabashin Syrte da nufin sarkake shi daga duk wata bazana 'yan ta'adan.
A nasa bangare wakilin mdd a kasar ta Libya shi ma yayi kira a wannan Talata ga dakarun gwamnatocin Libya dasu hada kai waje daya domin yakar kungiyar 'yan ta'adan na ISIS dake zamen babbar barazana ga kasar.
Yau watanni biyu kenan da gwamnatin hadaka ta Libya dake samun goyan bayan mdd dake da mazauni a Tripoli ta fara aiki, saidai har kawo yanzu ta kasa samun gindin zama saboda rikicin daya daidaita kasar tun bayan guguwar neman sauyin datayi awan gaba da mulkin tsohon shugaban kasar mirigayi kanal Ghadaffi a cikin shekara 2011.