Fada Da Ta'addanci A Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6463-fada_da_ta'addanci_a_libya
Sojojin Gwamnatin Hadin Kan Kasar Libya Suna Samun Galaba Akan 'Yan ta'adda.
(last modified 2018-08-22T06:58:25+00:00 )
Jun 09, 2016 02:10 UTC
  • Fada Da Ta'addanci A Libya

Sojojin Gwamnatin Hadin Kan Kasar Libya Suna Samun Galaba Akan 'Yan ta'adda.

Kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya ambato cewa; sojojin gwamnatin hadin kan kasa ta Libya suna kara samun nasara a cikin garin Sirt da ke hannun 'yan ta'addar kungiyar Isis.

Majiyar tsaron Libya ta ce; Sojojin Kasar Sun kuma kwace wani barikin soja wanda a baya ya ke karkashin ikon kungiyar ta Da'esh, ko Isil.

Tun a cikin watan da ya gabata ne dai sojojin kasar ta Libya da su ke a garin Misratah, su ka fara kai farmaki akan cibiyoyin kungiyar Da'esh. Kuma tun sojojin su ka kwace iko da barikin soja na al-jalidh da kuma yankin Bu Hadi a kusa da Srit.

Tun bayan kifar da gwamnatin Mu'ammar khaddafi a 2011 ne kasar ta Libya ta fada cikin fadace-fadace a tsakanin kungiyoyin da su ke dauke da makamai, da su ka hada da na 'yan'tadda.