Dakarun Gwamnatin Libiya sun kuza cikin Garin Syrte
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6508-dakarun_gwamnatin_libiya_sun_kuza_cikin_garin_syrte
Bayan gumurzu mai tsanani Dakarun Gwamnatin hadin kan kasar Libiya sun samu nasarar shiga garin Syrte dake hanun mamayar 'yan ta'addar ISIS.
(last modified 2018-08-22T06:58:25+00:00 )
Jun 09, 2016 23:39 UTC
  • Dakarun Gwamnatin Libiya sun kuza cikin Garin Syrte

Bayan gumurzu mai tsanani Dakarun Gwamnatin hadin kan kasar Libiya sun samu nasarar shiga garin Syrte dake hanun mamayar 'yan ta'addar ISIS.

Shugaban Gwamnatin hadin kan kasar Libiya Fa'iz Siraj ya sanar a wannan Alkhamis cewa a ci gaba da kokarin da Sojojin kasar keyi na yaki da 'yan ta'addar Da'esh ko kuma ISiS sun samu nasarar kutsawa garin Syrte dake a matsayin tungar 'yan ta'addar ISIS din .

Rahoton ya ce duk da cewa har yanzu ana ci gaba da musayar wuta tsakanun Dakarun tsaron Libiyan da mayakan ISIS a cikin garin Siyrte din, amma ana iya cewa Sojojin Libiya sun samu nasarar kwato garin.

Har ila yau Dakarun tsaron Libiyan sun 'yanto garin Harawa dake da nisan kilomita 70 daga Garin Syrte din.

Tun a watan da ya gabata ne Dakarun tsaron Libiyan suka fara aikin tsarkake gariruwan daga kalkashin mamayar kungiyar Da'esh ko ISIS a cikin kasar.

A yayin kaddamar da wannan runduna wacce aka yiwa lakabin Albunyanu-Marsus, Mayakan ISIS din sun yi karkuwa da fararen hula, inda suka hana su ficewa daga cikin garin.

Tun a shekarar da ta gabata ce Kungiyar ta ISIS ta mamaye garin Syrte a kasar ta Libiya inda ta mayar da shi babbar hedkotarta a cikin kasar.