Libya : (IS) Ta Kai Hare-hare Uku A Syrte
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6631-libya_(is)_ta_kai_hare_hare_uku_a_syrte
Rahotanni daga Libya na cewa kungiyar 'yan ta'adan (IS) ta kaddamar da wasu hare-haren kunar bakin wake guda uku kan dakarun gwamnatin hadaka na Libya a Syrte.
(last modified 2018-08-22T06:58:26+00:00 )
Jun 12, 2016 09:53 UTC
  • Libya : (IS) Ta Kai Hare-hare Uku A Syrte

Rahotanni daga Libya na cewa kungiyar 'yan ta'adan (IS) ta kaddamar da wasu hare-haren kunar bakin wake guda uku kan dakarun gwamnatin hadaka na Libya a Syrte.

kamar yadda kakakin cibiyar yada labarai na rundinar, Reda Issa ya shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP ya ce hare-haren sun janyo hasara rayukan mutane dayewa.

Bayanai sun nuna cewa an dai hare-haren ne har sau uku da mota a wannan Lahadin, kuma harin na farko an kai shi ne a kusa da wani taron dakarun masu goyan bayan gwamnati a dandalin Abou Habi dake kudu maso gabashi birnin Syrte dake gabashin Tripoli.

kazalika a cewar majiyar harin na biyu an kai shi ne a yammacin birnin a inda dakarun ke haduwa, yayin da na uku aka kai kan wani asibiti kauye dake a yankin.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun ke kokarin tsarkeke birnin na Syrte dage duk wata barazana kungiyar 'yan ta'adan.