Kamaru : Matsalar B.H Ta Jefa Dubban jama'a Cikin Matsalar Abinci
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6637-kamaru_matsalar_b.h_ta_jefa_dubban_jama'a_cikin_matsalar_abinci
MDD ta bayyana cewa hare-haren boko haram a Kamaru sun jefa dubban mutane cikin matsalar rashin abinci, wanda kuma a cewar ta babban abin damuwa ne.
(last modified 2018-08-22T06:58:26+00:00 )
Jun 12, 2016 11:45 UTC
  • Kamaru : Matsalar B.H Ta Jefa Dubban jama'a Cikin Matsalar Abinci

MDD ta bayyana cewa hare-haren boko haram a Kamaru sun jefa dubban mutane cikin matsalar rashin abinci, wanda kuma a cewar ta babban abin damuwa ne.

kimanin mutane 190.000 yanzu haka ke cikin hali kaka-ni-kayi a cewar babbar jami'ar kula da harkokin jin kai na MDD reshen Afrika, Najat Rochdi.

Jami'ar ta ce akwai bayanai dake nuna cewa 'yan boko haram sannu a hankali na kai hare-hare tare da kona kauyuka da gidaje da gonaki lokaci zuwa lokaci, wanda a cewar ta ke nuna cewa har yanzu fa ba'a gama murkushe kungiyar ba.

Ta ce lalle hare-harem jifa-jifa ne aman fa sannu a hankali suna daukan hankali.

kawo yanzu dai a cewar MDD yawan mutanen da matsalar rashin abinci ta shafa daga watan Janairu na wannan shekara ya haura daga dubu tara (900,000) zuwa Miliyam biyu da dari hudu (2,400,000).

Abun babban damuwa kuma a cewar Najat Rochdi, shi ne har yanzu ba'a kai ga hada kudaden da ake bukata ba don agazawa wadanda matsalar ta shafa, inda kawo yanzu kashi 30% ne kawai na kudade $ Miliyan 280 da ake bukata aka samu.