Dakarun Libiya Sun 'Yanto kudancin Ajdabiya
Dakarun tsaron Libiya bisa Jagorancin Janar Khalifa Haftar sun yanto yankin kudancin Ajdabiya bayan gumurzu mai tsanani tsakaninsu da mayakan 'yan ta'addar ISIS.
Tashar Telbijin din Almayadin dake watsa shirye-shiryanta daga Kasar Labnon ta habarta cewa majiyar tsaron kasar Libiya ta sanar da cewa Dakarun tsaron kasar dake yakar kungiyar ISIS bisa jagorancin janar Khalifa Haftar sun samu nasarar fatatakar mayakan kungiyar ISIS daga yankin kudancin Ajdabiya tare da tsarkake shi baya wani mumunar gumurzu a tsakaninsu.
Har ila yau Dakarun sun samun nasarar kwace iko da wasu sabin yankuna na cikin anguwanin Kawarisha da Kara Yunus dake birnin Bangazi.
A bangare guda Dakarun tsaron Gwamnatin hadin kan kasa sun samu nasarar dakile wani hari da mayakan ISIS din suka kai musu a garin Syrte tare da hallaka 10 daga cikinsu.
Tun a ranar 9 ga wannan wata na yuni da muke ciki ne Dakarun tsaron Gwamnatin hadin kan kasar da ake musu lakabi da Dakarun 12 ga watan Mayu suka shiga garin syrte da nufin tsarkake shi daga mayakan 'yan ta'addar na ISIS da suka mayar da shi babbar tungar su a kasar ta Libiya.