Libya: 'Yanto da kudancin garin Ajdabiya daga 'Yan ta'adda.
Jun 25, 2016 02:42 UTC
Sojojin Libya sun fatattaki 'yan ta'adda daga Kudancin Ajdabiya.
Tashar telbijin din al-mayadden ta bada labarin cewa; Sojojin gwamnatin Hadin Kan Kasa, a karkashin jagorancin Halifah Haftar, sun kwace kudancin birnin Ajdabiya bayan fada mai tsanani a tsakaninsu da 'yan kungiyar Da'esh.
A wasu sassan na gabacin kasar kamar alqawarisha, sojojin Libyan suna samun wasu nasarorin akan 'yan ta'addar. Tuni dai sojojin su ka kwace yankin Qar-Yunus da ke a Banighazi.
Dama tun da fari, sojojin kasar su ka shiga garin Sart bayan fada mai tsanani da 'yan kungiyar Da'esh.
Tags