An cimma Yarjejjeniyar tsagaita wuta a garin Derna na kasar Libiya
Dakarun tsaron Gwamnatin Libiya tare da Kungiyoyin 'yan tawaye sun cimma yarjejjeniyar tsagaita wuta a garin Derna dake gabashin kasar.
Majiyar labaran mahukuntan birnin Derna sun sanar da cimma yarjejjeniyar tsagaita wuta tsakanin Dakarun tsaron kasar tare da kungiyoyin dake dauke da makamai a garin.
Daga cikin sharudan wannan yarjejjeniya, wajibi ne kungiyoyin dake dauke da makamai su meka kansu ga Rundunar sojojin Gwamnatin hadin kan 'yan kasar.
Tun bayan Janyewar Mayakan 'yan ta'addar ISiS daga wasu anguwanin garin Derna a watan Avrilun da ya gabata, jiragen yakin Gwamnatin ta Libiya sun ci gaba da kai hare-hare, wanda ya yi babbar illa ga wasu manyan gine ginan kasar musaman ma babbar gadar yammacin garin da cibiyar wutar lantarki.
A bangare guda, Dakarun Gwamnatin Libiyan sun sanar da mutuwar Sojoji hudu tare jikkatar wasu 10 na daban a yayin gumurzu tsakanin su da mayakan ISIS.