Ziyarar Halifa Haftar A kasar Rasha
Jun 27, 2016 14:34 UTC
Kwamandan Sojan Libya Yana Ziyara A Kasar Rasha.
Kamfanin Dillancin Labarun Irna, ya ambato wata majiyar Rasha na cewa; Janar Khalifa Haftar ya fara ziyarar aiki a kasar Rasha.
Majiyar Rashan ta ci gaba da cewa; Janar Halifa Haftar zai gana da jami'an kasar Rasha akan yanayin da ake ciki a kasarsa dangane da fada da ta'addanci.
Gabanin isarsa kasar Rasha, Janar Haftar ya yada zango a birnin alkahira na kasar Masar inda ya gana da jami'an gwamnatinta.
Ziyarar tashi dai ta zo ne kwanaki kadan bayan da dakarunsa su ka yi nasarar korar 'yan ta'addar Da'esh daga kudancin Ajdabiya da ke gabacin kasar.
Tags