Libya: Sojoji Na Kara Samun Galaba Akan 'Yan ta'adda.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7549-libya_sojoji_na_kara_samun_galaba_akan_'yan_ta'adda.
Sojojin Libya Sun Kwace Iko da Wata Unguwa Mai Muhimmanci A Garin Sart.
(last modified 2018-08-22T06:58:32+00:00 )
Jul 02, 2016 08:01 UTC
  • Libya: Sojoji Na Kara Samun Galaba Akan 'Yan ta'adda.

Sojojin Libya Sun Kwace Iko da Wata Unguwa Mai Muhimmanci A Garin Sart.

Jaridar Ra'ayul-Yaum, ta ambato majiyar gwamnatin Libya na cewa; sojojin kasar sun kwace iko da unguwar 'sab'ami'ah' mai muhimmanci a cikin birnin Sart.

Bugu da kari majiyar ta ce; Sojojin suna ci gaba da nausawa zuwa asibitin 'Ibn Sina' da ke cikin birnin da kuma unguwar Ouagadougou da nan ne matattarar 'yan ta'addar kungiyar Da'esh, Isil.

Siraj Dho, wanda daya ne daga cikin kwamandojin sojojin kasar Libya ya ce; "Yan ta'addar Da'esh sun yi turjiya mai yawa, amma duk da haka sojoji sun yi nasarar kakkabe zaratan maharban da su ke da shi, tare kuma da kwace makamai masu yawa.