Gwamnatin Libiya Ta Jaddada Bukatar Wadata Ta Da Makamai Da Na'urar Yaki
Jakadan Kasar Libiya a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada bukatar ganin an hanzarta wadata gwamnatin Libiya da manyan makamai da kayayyakin aiki a fagen yakin da take yi da ta'addanci.
Jakadan Libiya a Majalisar Dinkin Duniya Ibrahim Addabashi ya jaddada bukatar ganin duniya ta hanzarta wadata rundunar sojin kasarsa da makamai na zamani gami da na'ura a fagen gudanar da ayyuka a yakin da ta daura da ayyukan ta'addanci a kasar. Yana mai fayyace cewa: Magance wannan annoba a Libiya yana bukatar tallafi daga dukkanin duniya musamman na makamai da na'urorin bincike.
Ibrahim Addabashi ya jaddada cewa; Libiya tana fuskantar duk wani nau'in annoban ta'addanci a cikin kasarta, kuma tana Allah wadai da duk wani salon aikin ta'addanci, sakamakon haka gwamnatin hadin kan kasa karkashin jagorancin fira minista Fa'yiz Sarraj da majalisar dokokinta suke fatan ganin dukkanin kasashen duniya sun goya musu baya a yakin da suka daura da duk wani nau'in ta'addanci a kasar misalin ayyukan ta'addancin kungiyar Da'ish, Al'Qa'idah, Ansarus- Shari'a da sauransu.