An cimma yarjejjeniyar farfado da kamfanin Mai A Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7576-an_cimma_yarjejjeniyar_farfado_da_kamfanin_mai_a_libiya
Magabatan Kanfanin Man fetur A Libiya sun cimma matsaya na farfado da kamfanin da nufin magance sabani da kuma kara yawan Man fetur din da kasar ke fitarwa
(last modified 2018-08-22T06:58:32+00:00 )
Jul 02, 2016 23:30 UTC
  • An cimma yarjejjeniyar farfado da kamfanin Mai A Libiya

Magabatan Kanfanin Man fetur A Libiya sun cimma matsaya na farfado da kamfanin da nufin magance sabani da kuma kara yawan Man fetur din da kasar ke fitarwa

A cikin wani bayyani da ta fitar ranar Assabar, Kamfani Man fetur din kasar Libiya ya ce bisa yarjejjeniyar da aka cimma an nada Mustapha Sun'ul.. a matsayin shugaban Kamfanin Man fetur din kasar da a baya yake rike da wannan matsayin kalkashin jagorancin Gwamntin hadin kan kasar dake birnin Tripoli, sai kuma Naji Almagribi a matsayin gungu cikin tawagar shugabanin kamfanin wanda yake a matsayin shugaban kamfanin kalkashin Gwamnatin kasar da hedkwata dake gabashin kasar.

A watan da ya gabata kungiyoyi da 'yan adawar kasar suka sanar da cewa an cimma matsayar farko kan kamfanin Man fetur din kasar saidai cimma matsaya na jagorancin Kamfanin na bukatar makunni.

Kasar Libiya dai na cikin gungun kungiyar OPEC , kuma matukar aka samu zaman Lafiya da konciyar hankali, kasar na iya kara yawan Man fetur din da take fitarwa a ko wata rana da ganga dubu 700.

Tun bayan faduwar Gwamnatin Marigayyi Kanal Mu'amar Kaddafi kasar ta fuskanci koma baya ga yawan danyan man fetur din da take fitarwa a ko wata rana, inda daga wancan lokacin zuwa yau,take fitar da ganga miliyon daya da dubu 600.

Masana siyasa na ganin cewa wannan yarjejjeniya da aka cimma na iya taimakawa Gwamnatin hakin kan kan kasar wajen tafiyar da milkin kasar.