Libya : An Bayar Da Belin Seifil- Islam Gaddafi
Rahotannin daga Libya na cewa an bayar da belin Seifil Islam Kaddafi dan tsohon shugaban kasar Muamar Ghaddafi a garin Zenten.
Lauyansa dan tsohon shugaban na Libya Karim Khan ne ya tabbatar da hakan, yana mai cewan anyiwa Seifil- Islam din afuwa tun a cikin watan Afrilu.
Lauyan dai yaki yin karin bayani akan inda Seifil- Islam din yake a halin yanzu.
kotun manyan laifuka ta duniya dai ta jima tana kira ga mahukuntan kasar Libya da su mika mata Seifil Islami Gaddafi domin hukunta shi, amma sabbin mahukuntan na Libya suka ci gaba da tsare shi domin ganin an gudanar da shari'arsa a cikin kasar.
Tun a cikin watan Yunin shekara ta 2011 ne kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ta fitar da sammacin kame Saiful Islam Gaddafi, tare da tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar Libya Abdullahi Sanusi, bisa zarginsu da kashe masu bore, wanda daga bisani ya rikide ya koma ayyukan tawaye, da hakan ya kai ga yi wa tsohon shugaban kasar Libya Mu'ammar Gaddafi kisan gilla a cikin watan Agustan 2011 a birnin Sirte.