Tashin Bom Ya Kashe Sojojin Gwamnatin Libiya Akalla 12 A Garin Benghazi
Wata mota da aka makare da bama- bamai ta tarwatse a garin Benghazi da ke arewa maso gabashin kasar Libiya, inda ta yi sanadiyyar mutuwar sojoji akalla goma sha biyu tare da jikkatan wasu da dama.
Rahotonni da suke fitowa daga Libiya a yau Alhamis suna bayyana cewa; Wata mota da aka cikata da bama - bamai ta tarwatse a tsakanin sojojin gwamnatin Libiya masu biyayya ga Janar Khalifa Haftar a garin Benghazi da ke shiyar arewa maso gabashin Libiya, inda sojojin akalla goma sha biyu suka rasa rayukansu, wasu da dama kuma suka jikkata.
Har ila yau wani jirgin saman soji mallakin gwamnatin Libiya da ke da matsuguni a garin Tabruk ya fadi a yammacin garin Benghazi kuma dukkanin sojojin da ke cikinsa sun mutu, sai babu bayanin dalilin faduwar jirgin.