Benjamin Netanyahu Ya Kusa Bakuntar Lahira A Kenya
Rahotanni daga kasar Kenya sun tabbatar da cewa jami'an tsaron kasar sun bankado wani shiri na halaka firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu a ziyarar da ya kai a kasar.
Wasu majiyoyin tsaro a kasar ta Kenya da suka bukaci a sakaya sunayensu, sun tabbatar da cewa a jiya jami'an tsaron Kenya sun sanar da masu tsaron lafiyar Netanyahu cewa an canja hanyoyin da zai bi zuwa masafkinsa daga filin safka da tashin jiragen sama na Nairobi, lamarin da ya jawo cacar baki a tsakanin jami'an tsaron Kenya da na Isra'ila tun kafin isowar Netanyahu, amma daga bisa jami'an tsaron Kenya sun tabbatar musu da cewa sun bakado wani shiri ne na tayar da bam a lokacin da Netanyahu zai wuce domin halaka shi.
Babban jami'i mai kula da tsare-tsaren tafiyar Netanyahu ya bayyana cewa, an samu canji a cikin mafi yawan abubuwan da aka shirya cewa Netanyahu zai gudanar a ziyararsa a kasar Kenya, dukkanin bangarorin biyu na Kenya da Isra'ila, suna ci gaba da yin rufa-rufa kan batun, tare da kin bayyana hakikanin abin da yake faruwa.