An Halaka 'Yan Ta'addan ISIS 10 A Gabshin Kasar Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7834-an_halaka_'yan_ta'addan_isis_10_a_gabshin_kasar_libya
Akalla 'yan ta'adda ISIS 10 ne suka halaka a kusa da birnin Sirte da ke gabashin kasar Libya.
(last modified 2018-08-22T06:58:34+00:00 )
Jul 09, 2016 01:20 UTC
  • An Halaka 'Yan Ta'addan ISIS 10 A Gabshin Kasar Libya

Akalla 'yan ta'adda ISIS 10 ne suka halaka a kusa da birnin Sirte da ke gabashin kasar Libya.

Rahotanni daga kasar ta Libya sun ce jami'an sojin kasar sun killace birnin Sirte babbar tungar 'yan ta'addan ISIS a kasar Libya, yayin da wasu daga cikin 'yan ta'addan su goma suka yi yunkurin satar hanya domin tserewa daga birnin, inda dakarun na Libya suka halaka su.

Tun a cikin watan Nuwamban shekara ta 2014 ce dai mayakan 'yan ta'addan ISIS daga kasashen duniya daban-daban musamman ma na larabawa, suka kwace iko da birnin Sirte mahaifar marigayi kanar Ghaddafi, kuma birnin na uku mafi girma a kasar ta Libya, inda suke da'awar cewa sun kafa abin da suke kira daular musulunci a birnin, wadda za ta ci gaba da bazuwa zuwa sauran yankunan Libya, daga nan kuma zuwa sauran kasashen Afirka.