Boko Haram ta sake kai wani hari a Kamaru
Mayakan boko haram sun sake kai wani harin ta'addanci a yankin arewacin kasar Kamaru
Kafar watsa labaran Afirka time ta nakalto Majiyar tsaron kasar Kamaru na cewa Akalla fararen hula biyu ne suka rasa rayukan su sanadiyar harin ta'addanci na kungiyar Boko haram a yankin Goulouzivini dake arewacin kasar a kusa da iyaka da Najeriya.
Majiyar tsaron ba tayi karin haske ba kan yadda aka kai harin, saida ta tabbatar da cewa za su ci gaba da aiyukan su na tsarkake arewacin kasar daga aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram
A bangare guda Manyan hafsoshin Soja na kasashen Najeriya , Nijer, Kamaru da Tchadi sun gudanar da taron su na farko jiya juma'a a garin Diffa na Jumhoriyar Nijer.
Taron manyan Hafsoshin Sojin na kasashen hudun dake fada da matsalar hare-haren ta'addanci na kungiyar Boko Haram ya tattaunawa ne kan yakin hadin gwiwar da Sojojin kasashen ke yi tare da Kunigiyar Boko haram kamar yadda Majiyar labaran kasar Nijer din ta sanar.
Har ila yau taron ya samu halartar Janar Lamidi Adeosun na Najeriya, wanda shi ne ke jagorantar rundunar hadin gwiwar kasashen dake yaki da kungiyar Boko Haram.