An kafa gwamnatin ceton kasa a Libiya
An kafa Gwamnatin ceton kasa da ta kumshi ministoci 18 a kasar Libiya.
A wani taron manema Labarai da suka kira, Firaministan kasar da yaunin nada ministocin ya rataya a kansa Fa'iz Assiraj da kuma Fathi Almujbiri kakakin Majalisar shugabancin kasar sun sana da kafa Gwamnatin ceton kasa wacce ta kumshi ministoci 18 daga cikin su a kwai Mata guda uku.
Almujbiri ya tabbatar da cewa A halin yanzu Al'ummar Libiya nada babban makiyi da ya kamata dukkanin 'yan kasar su hada kai domin yakar sa, kuma wannan babban makiyi ba kowa ba ne face ta'addanci.
Kakakin Majalisar shugabancin kasar ya bukaci dukkanin magabatan kasar da su kawo karshen cacar bakin da suke yi.
A bangare guda kuma Almujbiri ya bukaci kungiyoyin kasa da kasa da su taimakwa kasar a yakin da ta ke yi da aiyukan ta'addanci.
A yau Litinin ne za a kafa Majalisar kasar domin ta rantsar da sabuwar Gwamnatin ceton kasa