An Gano Wani Kabarin Gamagari A Kasar Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7969-an_gano_wani_kabarin_gamagari_a_kasar_libya
Sojojin kasar Libya sun gano wani kabarin gama gari a gabacin birnin Sirt
(last modified 2018-08-22T06:58:34+00:00 )
Jul 12, 2016 04:03 UTC
  • An Gano Wani Kabarin Gamagari A Kasar Libya

Sojojin kasar Libya sun gano wani kabarin gama gari a gabacin birnin Sirt

Majiyoyin sojojin kasar Libya sun bayyana cewa sojojin kasar na musamman wadanda ake kira "Katangar karfe" sun gano wani kabarin gama gari a gabacin birnin Sirt daga yammacin kasar.

Jaridar Al-yaumussabeh ta kasar Masar ta nakalto majiyar sojojin na cewa a jiya litinin ne sojojin suka gano wani kurkukun boye inda suka sami mutane biyu da ransu sannan suka gano wani kabarin gama gari kusa da shi, inda suka sami gawakin mutane 7 a cikinsa.

Majiyar ta kara da cewa akwai kekkyawan zaton cewa kungiyar Daesh ce ta kashe mutanen ta kuma bisnesu a cikin kabarin a lokacin da yakin gabacin birnin sirt yake karkashin ikonta.

Har'ila majiyar ta sojojin "Katangar karfe" ta bayyana cewa ana samun nasara a yakin da suke fafatawa da mayakan na kungiyar Daesh a birnin na Sirt mai tashar jiragen ruwa.