Makomar Libya Bayan Fitar Saiful Islam Ghaddafi Daga Gidan Kaso
A cikin wannan mako ne wata kotu a birnin Zantan na kasar Libya ta sanar da bayar da belin dan tsohon jagoran kasar marigayi Mu'ammar Ghadafi Saiful Islam Ghaddafi.
Wannan sanarwa dai ta zo ne a daidai lokacin da lamurra suke ta kara daukar salo daban-daban a kasar ta Libya, domin kuwa kasar tana cikin danbarwa tun daga shekara ta 2011 da masu adawa da Ghaddafi da suka hada da kabilun da ba su dasawa da shi da ke yankunan gabashin kasar, da kuma masu kishin addini da ke da alaka da alka'ida suka yi bore, daga karshe kuma NATO ta kawo karshen mulkin Ghaddafi, kafin daga bisani kuma aka shiga dambarwar siyasa a tsakanin 'yan adawa na siyasa da kuma masu ra'ayin alka'ida wadanda su ne gishikin 'yan tawayen da NATO ta mara wa baya wajen kifar da gwamnatin Ghaddafi tare da yi masa kisan gilla.
Saiful Islam tare da dan 'yan uwansa Mu'utasim Ghaddafi da kuma Khamis Ghaddafi sun kasance a sahun gaba wajen tunkarar masu bore da suka dauki makami tare da taimakon NATO da wasu daga cikin kasashen larabawa, an kashe mahaifinsu kanar Ghaddafi, kamar yadda kuma aka kashe Khamis da Mu'utasim, amma Saiful Islam ya fada a hannun 'yan tawayen Zantan a lokacin da yake kokarin tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar.
'Yan tawayen Zantan sun ki mika Saiful Islam ga sabbin mahukuntan Libya da ke Tripoli a lokacin, inda suka ci gaba da tsare shi a hannunsu, duk kuwa da cewa shi kansa ya yi farin cikin kasancewa a hannunsu, domin kuwa akwai kyakkyawar dangantaka a tsakaninsa da su tun lokacin da Ghaddafi ke mulki.
Sanar da bayar da belin na Saiful Islam wanda kotun Zantan ta yi, ya sa wasu daga cikin magoya bayansa a wasu yankunan kasar suna fitowa suna rera taken jinjina gare shi da kuma daga korayen tutoci na tsohuwar gwamnatin Ghaddafi, wanda a cikin shekaru biyu ko uku da suka gabata ba su isa su yi hakan ba, wanda kuma hakan ke nuni da cewa fitar da Saiful Islam daga gidan kaso, ya sake farfado da kumajin da magoya bayan marigayi Ghaddafi suke da shi na ganin an samu canji daga halin da kasar ta samu kanta a yanzu, bayan rawar da 'yan tawaye da NATO gami da wasu kasashen larabawa suk taka wajen hargitsa ta, musamman a halin yanzu da kungiyar 'yan ta'addan takfiriyyah wahabiyyah na ISIS suka fara kame wasu yankuna na kasar, wanda hakan shi ne abu mafi hadari ga kowa a kasar ta Libya, hatta ga su kansu tsoffin 'yan tawayen da kuma 'yan siyasa da suke rike da madafun iko.
Ko shakka babu ganin irin halin da aka jefa kasar Libya a ciki, kasantuwar Saiful Islam a waje zai zama yana da babban tasiri ga lamurra da dama da suke da alaka da makomar kasar, domin kuwa akwai kabilu da dama da suke a shirye su mara masa baya domin samar da wani canjin na daban a kasar, musamman ma su kansu kabilun Zantan wadanda suka dandana kudarsu a Triploi a hannun 'yan tawaye na Fajr Libya da kuma 'yan tawayen Misratah a cikin 2014, wanda hakan ya tilasta ma mayakan Zantan janyewa daga Tripoli baki daya.
Duk kuwa da cewa a wasu yankunan gabashin kasar Libya Saiful Islam ba zai samu magoya baya ba musamman ma a Benghazi da Misratah, amma zai samu goyon bayan kabilun Sirte da kuma Warfala da ke birnin Bani Walid, gami da kabilar Kazazifah da kabilun Sabha da ke kudancin kasar.
Ko shakka babu, ba abu ne mai sauki 'yan siyasar Libya da tsoffin 'yan tawayen kasar su amince da wannan mataki na bayar da belin din Saiful Islam da kotun Zantan ta dauka ba, domin kuwa hakan zai saka su cikin hali na gaba kura baya sayaki, domin kuwa a halin yanzu suna fuskantar babban hatsari na kungiyar 'yan ta'aaddan ISIS, a lokaci guda kuma suna kallon sakin Saiful Islam a matsayin wata barazana gare su, wadda ta yi kama da dawowar kanar Ghaddafi, wanda kuma hakan ne ma ya sanya 'yan siyasa a Tripoli suka fito suka karyata cewa an bayar da belin na Saiful Islam.
To ko ma dai mene, kwanaki masu zuwa ne za su iya fayyace makomar lamurra a Libya bayan fitar Saiful Islam Ghaddafi daga gidan kaso.