Libiya: An Sake Dage Shari'ar Saadi Ghaddafi
Kotu a Libiya ta sake dage shari'ar Sa'adi Ghadaafi har zuwa farkon watan oktoba na wannan shekara.
Dan tsohon shugaban kasar ta Libiya Sa'adi Ghadaffi ya dai shafe tsawon shekaru biyu yana jiran a yi masa shari'a.
Wata majiyar tsaron gidan kason birnin Tripoli inda ake tsare da Saadi Ghaddafin, ta shaidawa masu aiko da rahotanni cewa an dage shari'a bisa bukatar lawyoyi masu bada kariya ga Sa'adin din da basu samu damar halartar zaman kotun ba.
Shi dai Saadi Ghaddafi ana zargin shi ne da hada baki wajenkashe masu zanga-zanga a lokacin guguwar neman sauyi da ta yi sanadiyyar hanbare mahaifinsa kan madafun iko a cikin shekara 2011.
Hukumomin Nijar ne dai suka mika Saadi Ghaddafi ga hannun hukumomin Libiya a ranar 6 ga watan Maris na 2014, bayan shafe tsawan lokaci yana gudun hujira a kasar.