An Hallaka Shugaban Alka'ida A Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8086-an_hallaka_shugaban_alka'ida_a_libiya
Dakarun Sojin Saman Libiya sun sanar da hallaka wani babban komandar kungiyar Alka'ida
(last modified 2018-08-22T06:58:35+00:00 )
Jul 13, 2016 13:14 UTC
  • An Hallaka Shugaban Alka'ida A Libiya

Dakarun Sojin Saman Libiya sun sanar da hallaka wani babban komandar kungiyar Alka'ida

A wata sanarwa da suka fitar a wannan Laraba, Dakarun Sojin Saman na Libiya sun sanar da hallaka Ibrahim Asheikh shugaban kungiyar Alka'ida a yankin Raqtat dake gabashin Ajdabiya.

Ibrahim Ashekh shine shugaban wata Kungiyar ta'addanci mai suna Sarayah Addifa'a da kuma ta kasance kalkashin kungiyar Alka'ida a birnin Bangazi na kasar Libiya, an hallaka shi a yayin hare-haren da Dakarun saman Libiyan ke ci gaba da kaiwa kan sansanin kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin kasar.

A baya ma Dakarun na Libiya sun sanar da jikkata ibrahim Ashekh a wani gumurzu tsakanin su da mayakan 'yan ta'addar na Alka'ida a birnin Bangazi.

Tun bayan faduwar Gwamnatin marigayi Kanal Mu'amar Kaddafi a shekarar 2011, Kasar Libiyan ta zamanto wata tunga ta kungiyoyin 'yan ta'adda daga cikin kuwa har kungiyar ta'addancin nan ta ISIS wacce ta kasance babbar barazana ga zaman lafiyar Duniya.