Boko Haram ta kai hari a arewacin Kamaru
Majiyar tsaron kasar Kamaru ta sanar da mutuwar fararen hula sanadiyar harin mayakan boko haram a arewacin kasar
Kafar watsa labaran Afirka time ta nakalto majiyar tsaron kasar Kamaru na cewa A jiya Talata mayakan kungiyar Boko haram sun kai harin ta'addanci a kauyen Maloumri dake yankin Kolofata na arewacin kasar kusa da iyaka da Najeriya.
Majiyar ta ce ko baya ga fararen hula biyun da mayakan kungiyar boko haram din suka kashe, sun kone gidajen mazauna kauyen da dama sannan kuma sun fasa shaguna inda suka kwashi abinci.
A kwanakin baya-bayan nan Arewacin kasar ta Kamaru na fuskantar hare-haren ta'addanci na kungiyar Boko Haram musamam ma hare-haren kunan bakin wake.
A ranar 30 ga watan yunin da ya gabata, wani dan kunar bakin wake da ake kautata zaton dan boko haram ne ya kai harin kunan bakin wake a garin Djakana dake arewacin kasar, inda mutane 11 suka rasa rayukansu.
Baya ga kahan a ranar Juma'ar da ta gabata kimanin Mutane 7 ne suka rasa rayukansu sanadiyar harin na boko haram a wani gari dake kan iyakar kasar da Najeriya, sannan kuma da dama daga cikin mazauna garin sun gudu domin tsira da rayukansu.