Sojojin Kasar Faransa Guda Biyu Sun Rasa Rayukansu A Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8374-sojojin_kasar_faransa_guda_biyu_sun_rasa_rayukansu_a_libya
Rahotanni daga kasar Libya sun ce sojojin kasar Faransa biyu sun halaka a kusa da birnin Benghazi da ke gabashin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:37+00:00 )
Jul 20, 2016 06:51 UTC
  • Sojojin Kasar Faransa Guda Biyu Sun Rasa Rayukansu A Libya

Rahotanni daga kasar Libya sun ce sojojin kasar Faransa biyu sun halaka a kusa da birnin Benghazi da ke gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Sporting ya bayar da rahoton cewa, an harbo wani jirgin yakin kasar Faransa mai safkar angululu a kusa da birnin Benghazi, inda biyu daga cikin sojojin kasar ta Faransa suka mutu, wata kungiyar 'yan tawayen Libya da ke dauke da makamai a Benghazi ta ce ita ce ta kakkabo jirgin.

A kwanakin baya ne Faransa ta aike da dakarunta a asirce zuwa gabashin birnin Benghazi domin taimaka ma janar Khalifa Haftar wajen yaki da 'yan kungyar ISIS, wadanda suke hankoron kwace iko da birnin na biyu mafi girma a Libya.