Libya Ta Zargi Faransa Da Keta Hurumin Kasar Ta
Gwamnatin hadaka ta Libya ta zargi Faransa da keta hurumin kasar ta, bayan sanarwar hukumomin Paris na cewa sojojinta Faransa uku sun mutu a Libya, bayan da aka harbo jirgi mai saukar ungulun da suke ciki.
Wata sanarwa da gwamnatin Libya ta wallafa a shafin ta na facebook ta ce abun allawadai ne kuma keta hurumin kasar ne abunda faransa ta yi ba tare da wata hujja ba ko kuma amuncewar kasar.
Rahotanni daga Libya sun nuna cewa daririwan mutane ne sukayi zanga-zanga a sassa daban daban na kasar don nuna kyammarsu ga kasancewar sojojin Faransa a Libya.
Da safiyar ranar Laraba ne, kakakin ma'akatar tsaron Faransan, Stephane Le Foll , a karon farko ya tabbatar da cewa dakarun Faransa na musamman sun mutu a Libya a lokacin da suke tsaka da bautawa kasa.
Har yanzu dai babu wata kungiya data dau alhakin kakkabo jirgin na Faransa.