Libya: Jiragen Yakin Faransa Sun Kai Hari A Kusa da Banighazi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8476-libya_jiragen_yakin_faransa_sun_kai_hari_a_kusa_da_banighazi
Harin na jiya da Jiragen Yakin Faransan Su ka kai a Banighazi ya yi sanadin mutuwar 'yan ta'adda 16, tare kuma da tilasta musu ja da baya.
(last modified 2018-08-22T06:58:38+00:00 )
Jul 22, 2016 02:03 UTC
  • Libya: Jiragen Yakin Faransa Sun Kai Hari A Kusa da Banighazi

Harin na jiya da Jiragen Yakin Faransan Su ka kai a Banighazi ya yi sanadin mutuwar 'yan ta'adda 16, tare kuma da tilasta musu ja da baya.

Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua ya nakalto cewa; Jiragen yakin Faransa sun kai hari a kusa da birnin Banighazi a jiya alhamis.

Rahoton ya kuma ce; harin na jiya ya yi sanadin mutuwar 'yan ta'adda 16, tare kuma da tilasta musu ja da baya.

Wannan harin na Faransa ya zo ne a daidai lokacin da al'ummar kasar ta Libya su ke yin zanga-zangar yin tir da yadda Faransa ta ke tsoma baki a harkokin cikin gidansu.

Ita ma gwamnatin hadin kan kasar ta Libya ta fitar da wani bayani na nuna kin amincewa da shigar sojojin Faransa cikin kasar.

A ranar laraba ne dai Faransan ta sanar da mutuwar wasu sojojinta da ta ce suna aiki ne a cikin libya.