Libiya Ta Fayyace Aikin Dakarun Kasashen Waje Da Zata Jibge A Kasarta
Kwamandan rundunar sojin saman kasar Libiya ya bayyana cewa; Aikin rundunonin sojin Amurka, Birtaniya da Faransa a Libiya shi ne sanya ido kan kai komon mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish domin samun damar murkushe su.
A jawabin da ya gabatar dangane da batun jibge rundunonin sojin kasashen Amurka, Birtaniya da kuma Faransa a sansanin sojin sama na Banina da ke garin Benghazi na kasar Libiya: Babban kwamandan sojin saman gwamnatin Libiya Saqar Ajjarushi ya yi da'awar cewa: Sojojin kasashen uku ba zasu shige 20 ba, kuma aikinsu shi ne sanya ido kan kai komon 'yan ta'addan kungiyar Da'ish da kuma gano rumbunan makamansu.
Ajjarushi ya kara da cewa: Gwamnatin Libiya zata kara fadada ayyukan irin wadannan sojojin kasashen waje a sauran yankunan kasarta musamman Tabruk, Misratah da Tripoli fadar mulkin kasar da nufin samun saukin dakile ayyukan ta'addanci a kasar.