Harin Bam ya hallaka Mutane 22 a Kasar Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9064-harin_bam_ya_hallaka_mutane_22_a_kasar_libiya
Akalla Mutane 22 ne suka mutu sanadiyar tashin Bam a birnin Bangazi dake gabashin Libiya
(last modified 2018-08-22T06:58:42+00:00 )
Aug 03, 2016 00:56 UTC
  • Harin Bam ya hallaka Mutane 22 a Kasar Libiya

Akalla Mutane 22 ne suka mutu sanadiyar tashin Bam a birnin Bangazi dake gabashin Libiya

Wata mota shake da bama-bamai da aka kai hari da ita kan jami'an tsaro a birnin Benghazi da ke gabashin Libya ta yi sanadin mutuwar Mutane 22 tare da jikkata wasu 20 na daban

An dai kai wannnan harin ne bayan kwana guda da jiragen yakin Amurka suka kai hari kan mayakan IS a birnin Sirte.

Wata majiyar tsaro a birnin Benghazi ta bayyana cewa an kudiri kai harin ne kan hedikwatar ruduna ta 146 ta sojojin Libya, wadanda ke dauki-ba-dadi da kungiyoyin masu tada-kayar-baya a birnin Benghazin.

Bama-baman sun tarwatse ne a kusa da wani gidan mai a  gundumar Kawarisha da ta zama fagen-daga, inda aka yi ta tabka kazamin fada.

Kungiyar masu ta tada-kayar-baya da ke ikirarin juyin-juya-hali ta Benghazi Revolutionary Shura Council ta fito fili ta dauki alhakin kai hari ta hanyar yin bayani a wani dandalin sada zumunta na Twitter da ake dangantawa da kungiyar.

Wannan kungiya dai wani bangare ne na gamayar  kungiyoyin masu tada kayar baya a kasar ta Libya da suka yi mubaya'a ga kungiyar IS.

Wasu kafafen yada labarai sun ce harin ya ritsa da wasu sojojin kasar, A baya baya nan dai Garin Bangazi na fuskantar hare-haren bama-bamai a kan Dakarun tsaron kasar.

Tun bayan faduwar Marigayyi Kanal Mu'amar Kaddafi a shekarar 2011, kasar Libiya ke fuskantar rashin tsaro, inda kungiyoyin 'yan ta'adda suka yi amfani da wannan dama na rashin Gwamnati suka kame wasu yankuna na kasar.