Jami'an Tsaron Nijar Sun Kama Wasu Kusoshin Boko Haram A Kasar
Rundunar sojin Jamhuriyar Nijar sun sanar da samun nasarar kame wasu kusoshin kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram da ta addabi kasar cikin watannin da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran Xianhua na kasar China ya sanar da cewa a jiya Laraba ce cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta Nijar ta fitar ta sanar da cewa dakarunta sun sami nasarar cafke wasu mutane guda biyu da suke samar wa 'yan Boko Haram din kayayyakin abinci da makamashin da suke bukata a yankin Garin Dogo da ke kusa da yankin Diffa da ke kudu maso gabashin Jamhuriyar ta Nijar.
Rahotannin sun ce hakan wani ci gaba ne da sojojin suka samu a fadan da suke yi da 'yan kungiyar ta Boko Haram wadanda suka addabi kasar musamman tun daga shekarar bara ta 2015 zuwa yanzu.
Nijar dai tana daga cikin kasashen yammacin Afirka da suka hada da Nijeriya, Kamaru da Chadi da suke fama da hare-haren kungiyar Boko Haram din.