Yan Bindiga Sun Sace 'Yan Kasar Masar 27 A Kasar Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9337-yan_bindiga_sun_sace_'yan_kasar_masar_27_a_kasar_libiya
Wasu gungun 'yan bindiga sun sace 'yan kasar Masar 27 a yankin Albariqah na kasar Libiya.
(last modified 2018-08-22T06:58:44+00:00 )
Aug 08, 2016 05:32 UTC
  • Yan Bindiga Sun Sace 'Yan Kasar Masar 27 A Kasar Libiya

Wasu gungun 'yan bindiga sun sace 'yan kasar Masar 27 a yankin Albariqah na kasar Libiya.

Shafin Bawabatul- Fajir ya habarto daga kakakin gwamnatin rikon kwaryar kasar Libiya Khatam Al-Aribi cewa; Wasu gungun 'yan bindiga da suka rufe fuskokinsu da kyalle sun sace 'yan kasar Masar 27 a yankin Albariqah na kasar Libiya.

Al-Aribi ya kara da cewa: Jami'an tsaron Libiya suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano yadda aka boye mutanen da aka sace gami da mutanen da suke da hannu a sace su.

A gefe guda kuma kakakin ma'aikatar harkokin wajen Masar Ahmad Abu-Zaid ya bayyana cewa ba su da cikakken labarin kan sace 'yan kasar ta Masar amma sun bukaci karin haske daga bangaren gwamnatin rikon kwaryar Libiya kan batun.