Sojojin Kasar Libya Na Kara Samun Nasara Akan Da'esh
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9424-sojojin_kasar_libya_na_kara_samun_nasara_akan_da'esh
Sojojin Libya Suna Kara Kutsawa A cikin Sirt
(last modified 2018-08-22T06:58:44+00:00 )
Aug 10, 2016 14:36 UTC
  • Sojojin Kasar Libya Na Kara Samun Nasara Akan Da'esh

Sojojin Libya Suna Kara Kutsawa A cikin Sirt

A yau laraba sojojin gwamnatin hadin kan kasar Libya sun sake kutsawa cikin garin Sirt da ke hannun Da'esh.

Kamfanin Dillancin Labarun Reuters daga kasar ta Libya ya ambato cewa; Sojojin na  kasar Libya sun kame wata cibiya ta nazari da bincike a cikin birnin,  bayan korar 'yan kungiyar ta Da'esh daga cikinta.

Kakakin sojan kasar ta Libya Ridha Isa ya ce; Dakarunmu sun sami nasarar kwace cibiyar bincike ta Ougadugou da kuma asibiti da jami'ar birnin na Sirt.

Sojojin gwamnatin kasar ta Libya dai suna son kwace garin ne na Sirta daga hannun 'yan kungiyar ta Da'esh da ta kafa iko a cikinsa.