Amurka ta tabbatar da Dakarunta a kasar Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9490-amurka_ta_tabbatar_da_dakarunta_a_kasar_libiya
Kakakin Ma'aikatar tsaron Amurka ya tabbatar da tura Sojojin kasar na musaman zuwa kasar Libiya
(last modified 2018-08-22T06:58:45+00:00 )
Aug 11, 2016 14:32 UTC
  • Amurka ta tabbatar da Dakarunta a kasar Libiya

Kakakin Ma'aikatar tsaron Amurka ya tabbatar da tura Sojojin kasar na musaman zuwa kasar Libiya

A wani taron manema labarai da ya kira a wannan Alkhamis, kakakin Pentagone Henrietta Leavitt ya tabbatar da Sojojin Amurka na musaman wadanda ake kira da Komando a kasar Libiya inda ya ce suna taimakawa Dakarun Libiyan a yaki da suke yi da kungiyar IS a birnin Sirte.

Kakakin na Pentagon ya ce Dakarun tsaron Amurkan na taimakawa Gwamnatin hadin kan kasar ne kuma suna bayar da shawarwari ne kan yadda za a kawo karshen kungiyar 'yan ta'adda a Libiya, amma ba sa shiga yakin da ake kobzawa kai tsaye a birnin na Syrte.

Henrietta Leavitt ya kara da cewa ko baya ga wannan Sojojin na Amurka na taimakawa Dakarun Libiyan wajen musayar bayyanai, musaman ma a yankunan da ake rikici tsakanin Dakarun tsaron kasar da 'yan bindiga wadanda suke  nesa na manyan buranan kasar.

Wannan sanarwa na zuwa ne a yayin da  Dakarun tsaron Libiya suka  sanar da gagarumar nasarar  da suka  ce sun samu a garin Sirte, Kakakin ofishin sadarwa na Dakarun tsaron Libiya Ridha Isa ya sanar a jiya Laraba cewa Dakarun tsaron kasar sun samu nasarar kwato babbar cibiyar kasuwancin nan ta garin Sirte da kuma Asibitoci gami da jami'ar garin daga hanun 'yan ta'addar IS, wannan dai babbar nasara ce da dakarun tsaron Libiyan suka samu a cikin 'yan kwanakin nan.