Sakin 'Yan Kasar Masar 23 Da Aka Sace A Kasar Libiya
Majiyar kasar Masar ta sanar da sakin 'yan kasarta 23 da wasu 'yan bindiga suka sace su a kasar Libiya a kwanakin baya.
Sojojin gwamnatin kasar Libiya sun samu nasarar 'yantar da 'yan kasar Masar 23 da wasu 'yan bindiga suka sace a yankin Bariqah na kasar ta Libiya a makon da ya gabata.
Majiyar tsaron Libiya ta sanar da cewa; Bayan killace yankin na Bariqah tare da gudanar da bincike sojojin kasar sun samu nasarar gano yadda ake tsare da 'yan kasar ta Masar inda suka kwato su daga hannun 'yan bindigan, kuma babu wanda ya rasa ransa a kokarin yantar da su.
A halin yanzu haka yan kasar ta Masar sun isa gida dauke da tutocin kasarsu cikin murna inda suka samu tarba daga jami'an kasar da iyalansu