Sojojin Gwamnatin Libya Sun Kwace Gidan Radiyon Birnin Sirt
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9613-sojojin_gwamnatin_libya_sun_kwace_gidan_radiyon_birnin_sirt
Sojojin Gwamnatin Hadin Kan Kasar Libya Sun Karbi Iko da Gidan Rediyon Garin Sirt daga hannun 'Yan ta'adda.
(last modified 2018-08-22T06:58:45+00:00 )
Aug 14, 2016 10:22 UTC
  • Sojojin Gwamnatin Libya Sun Kwace Gidan Radiyon Birnin Sirt

Sojojin Gwamnatin Hadin Kan Kasar Libya Sun Karbi Iko da Gidan Rediyon Garin Sirt daga hannun 'Yan ta'adda.

Sojojin Gwamnatin Hadin  KanKasar Libya Sun Karbi Iko da Gidan Rediyon birnin Sirt daga hannun 'yan ta'adda.

Kamfanin dillancin labarun Anatoli na kasar Turkiya, ya ambato majiyar tsaron kasar Libya daga birnin Tripoli na cewa; A jiya asabar ne sojojin kasar su ka yi nasarar korar 'yan ta'addar kungiyar Da'esh daga ginin gidan rediyon birnin Sirt.

A tsawon lokacin da kungiyar ta Da'esh ta ke rike da gidan Rediyon ta rika amfani da shi domin watsa shirye-shiryenta.

A kwanaki kadan da su ka gabata ma dai sojojin gwamnatin hadin kan kasar ta Libya sun yi nasarar kwace jami'a da kuma asibiti daga hannun Da'esh daga cikin garin na Sirt.

A cikin watan Mayu ne dai sojojin libyan suka fara kai farmaki a garin Sirt da zummar kwace shi daga hannun 'yan ta'adda.