Gargadin Majalisar Dinkin Duniya Kan Yanayin 'Yan Gudun Hijira A Kasar Uganda.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi da kuma nuna tsananin damuwarta dangane da yanayin da 'yan gudun hijira su ke ciki a kasar Uganda.
Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua na kasar Sin, ya ambato mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniyan, Farhan Haq yana cewa; Da akwai 'yan gudun hijira 200,000 a kasar Uganda da suke bukatar taimakon kasa da kasa, da su ka hada da na abinci.
Kakakin MDD ya kara da cewa sakamakon rashin kudi an samu raguwar irin taimakon da ake ba wa wadannan 'yan gudun hiijirar da kashi 50 cikin dari.
Sanarwar ta yi ishara da cewa; A kowane wata, hukumar samar da abinci ta duniya tana da bukatar dalar Amurka miliyan 7 domin wadata 'yan gudun hijirar da abinci.
Sabon rikicin da ya barke a kasar Sudan ta kudu a tsakanin shugaban kasa Silva Kiir da tsohon mataimakinsa Reik Machar ya taimaka wajen kara kwararar dubban 'yan gudun hijira zuwa kasar Uganda.