Kamaru : Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane Uku
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9931-kamaru_harin_kunar_bakin_wake_ya_kashe_mutane_uku
Rahotanni daga Kamaru na cewa mutane a kalla uku ne suka rasa rayukan su, kana wasu kimanin 20 suka raunana sakamakon wani harin kunar bakin wake a yankin arewa mai nisa.
(last modified 2018-08-22T11:28:48+00:00 )
Aug 21, 2016 11:10 UTC
  • Kamaru : Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane Uku

Rahotanni daga Kamaru na cewa mutane a kalla uku ne suka rasa rayukan su, kana wasu kimanin 20 suka raunana sakamakon wani harin kunar bakin wake a yankin arewa mai nisa.

Wata majiyar tsaro data bukaci a sakaya sunan ta, ta shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP cewa maharin ya zo ne kan babur, kuma ya tarwatsa kansa a wata gada dake kusan kasuwar garin ''Mora''.

Birnin ''Mora'' dai ya kunshi barikin sojin hadaka na kasashen yankin tafkin Chadi dake yaki da kungiyar boko Haram.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya data dau alhakin kai harin, saidai sau tarin yawa akan danganta ire ire wadanan ayyukan ta'adi ga kungiyar nan da aka fi sani da Boko haram.