An Kashe Sojojin Kasar Libiya A Yankin Arewa Maso gabacin kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9970-an_kashe_sojojin_kasar_libiya_a_yankin_arewa_maso_gabacin_kasar
Rahotanni na kasashen larabawa da dama sun bayyana cewa an kashe sojojin kasar a arewa maso gabacin kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:48+00:00 )
Aug 22, 2016 01:53 UTC
  • An Kashe Sojojin Kasar Libiya A Yankin Arewa Maso gabacin kasar

Rahotanni na kasashen larabawa da dama sun bayyana cewa an kashe sojojin kasar a arewa maso gabacin kasar

Kamfanin dillancin labaran Irna ya bayyana cewa an kashe sojojin Halifa Aftar 6 sanadiyyar tashin boma bomai a jiya Lahadi. 

Labarin ya kara da cewa bom din ya tashi ne a yankin Qawareshe daga yammacin birnin Bangazzi babban birnin yankin gabacin kasar.

A ranar talatan da ta gabata ma wasu labarai sun bayyana cewa na kashe sojojin Janar Haftar mai ritaya guda 38. a dai lokacin da suka shiga fafatawa da sojojin  kungiyar majalisar shuran juyin juya hali na Bengazi.

Tun bayan faduwar gwamnatin Mo'ammar Kazzafi a shekara ta 2011 ne kasar Libiya ta shiga yakin basasa wanda ya kai ga tabarbarewar harkokin tsaro a kasar. A cikin farkon wannan shekarar ne, tare da shigar majalir dinkin duniya aka sami kafa gwamnatin hadin kan kasa tsakanin kungiyoyin yan siyasa wadanda basa ga maciji na juna.