-
Amurka Ta Hallaka Mayakan Al-Shabab 27 A Somaliya
Jun 05, 2018 11:29Rundunar sojin Amurka ta ce harin da dakarunta na musammam suka kai ta sama, ya hallaka mayakan al-Shabab 27 a arewacin Somaliya.
-
Nijar : 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Kashe Mutum 6 A Diffa
Jun 05, 2018 11:09Hukumomi a Jamhuriya Nijar sun sanar da mutuwar mutane 6, da kuma raunanar wasu 37 a wasu jerin hare haren da wasu 'yan kunar bakin wake uku suka kai a jihar Diffa dake kudu maso gabashin kasar, kusa da kan iyakar Najeriya.
-
Sojojin Najeriya Sun Kwato Mutane 148 Daga Garkuwan Mayakan Boko Haram A Jihar Borno
Jun 05, 2018 07:24Kakakin sojojin Najeriya ya bayyana cewa sojojin kasar sun sami nasarar kwato mutane 148 daga garkuwan mayakan boko haram daga ciki har da mata 58 da kuma yara 75.
-
Sojojin Libiya Karkashin Jagorancin Janar Haftar Sun Fara Kuntsa Kai Cikin Garin Darna
Jun 05, 2018 01:50Sojojin Libiya karkashin jagorancin Janar Khalifa Haftar sun fara 'yantar da wasu yankunan garin Darnah da ke gabashin kasar.
-
An Kame Wasu Daga Cikin Fursunoni Sama da 200 Da Suka Gudu A Minna, Nijeriya
Jun 04, 2018 13:52Ma'aikatar cikin gidan Nijeriya ta sanar da cewa jami'an tsaro sun sami nasarar sake kame wasu fursunoni 30 daga cikin fursunoni 219 da suka gudu daga wani gidan yari da ke garin Minna, na jihar Niger a Nijeriyan a daren jiya.
-
Firayi Ministan Kasar Madagaska Yayi Murabus Daga Mukaminsa
Jun 04, 2018 13:51Firayi ministan kasar Madagaska, Olivier Mahafaly, ya sanar da yin murabus dinsa don girmama umurnin da kotu ta bayar na kafa gwamnatin hadin kan kasa a kasar da nufin kawo karshen rikicin siyasa da ya kunno kai a kasar.
-
Dangote Ya Bawa Yansandan Najeriya Mutocin Sintiri 150
Jun 04, 2018 07:27Cibiyar Aliko Dangote Faudation mallakin hamshakin dan kasuwa a tarayyar Nigeria ya bada kyautan motocin sintiri 150 ga hukumar yansandan Najeriya.
-
Najeriya:'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 13 A Jahar Benue.
Jun 04, 2018 01:58Hukumomin jahar Benue sun sanar da hallakar mutum 13 sanadiyar wasu tagwayen hare-hare da 'yan bindiga suka kai kauyukan dake cikin jahar
-
Shugaba Ouatara Na Son Tsayawa Takara Karo Na Uku
Jun 04, 2018 01:57Shugaban Cote d’Ivoire Alassane Dramane Ouattara ya ce bai kawar da yiyuwar sake tsayawa takarar shugabancin kasar karo na uku ba a shekara ta 2020.
-
An Ceto Bakin Haure 67 A Gabar Ruwan Tunusiya
Jun 04, 2018 01:57Ma'aikatar tsaron kasar Tunusiya ta sanar da cewa jami'an tsaron ruwan kasar sun ceto bakin haure 76 a gabar ruwan kudancin kasar.