Janar Suleimani: An Kirkiro Da’esh Ne Don Raunana Kasar Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i12064-janar_suleimani_an_kirkiro_da’esh_ne_don_raunana_kasar_iran
Kwamandan dakarun Qudus na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Manjo Janar Qassem Suleimani ya bayyana cewar and kirkiro kungiyar Da’esh da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda masu kafirta mutane ne da nufin raunana kasar Iran.
(last modified 2018-08-22T11:29:02+00:00 )
Oct 06, 2016 10:58 UTC
  • Janar Suleimani: An Kirkiro Da’esh Ne Don Raunana Kasar Iran

Kwamandan dakarun Qudus na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Manjo Janar Qassem Suleimani ya bayyana cewar and kirkiro kungiyar Da’esh da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda masu kafirta mutane ne da nufin raunana kasar Iran.

Janar Suleimani ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi wajen bikin tunawa da shekara guda shahadar daya daga cikin manyan kwamandojin dakarun kare juyin juya halin Musulunci Birgediya Janar Hossein Hamedani a wani hari da ‘yan kungiyar ta’addancin nan ta Da’esh suka kai masa Siriya, inda ya ce ba an kirkiri kungiyar Da’esh da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda don yaki a Siriya ba ne, face dai sai don cutar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Janar Suleimani ya kara da cewa gwamnatin Siriya ta hanyar taimakon da take samu daga Iran ta samu nasarar tsayin dakan daga mamayar wadannan ‘yan ta’adda na tsawon shekaru biyar, yana mai cewa aikin da dakarun Iran suke yi a Siriya wani lamari da yake ba da kariya ba wai kawai ga kasashen larabawa, face dai har da Iran da kuma sauran kasashen musulmi.

Tun a shekara ta 2011 ne kasar Siriya ta ke fuskantar hare-haren ta’addancin kungiyoyin ‘yan ta’addan da aka shigo da su kasar daga kasashen waje lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 400,000.