Iran Ta Sake Jaddada Goyon Bayanta Ga Al'ummar Palastinu
Jamhuriyar Musulunci ta Iran sake jaddada goyon bayanta ga al'ummar kasar Palastinu a kokarin da suke yi na 'yantar da kansu daga mamayan yahudawan sahyoniya kamar yadda ta nuna damuwarta ainun da irin ci ga da rikon sakainar kashin da cibiyoyin kasa da kasa suke yi wa lamarin Palastinu da kuma ci gaba da gina matsugunan yahudawa da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta ke yi.
Mataimakin jakadan kasar Iran din a Majalisar Dinkin Duniya Gholam-Hossein Dehqani ne ya bayyana hakan a wani jawabi da yayi a babban zauren MDD inda kokarin da kasashen duniya suke yi wajen dakatar da ci gaba da gina matsugunan yahudawa da HKI take yi ya ci tura sakamakon rashin daukan matakan da suka dace kan sahyoniyawan da ba a yi ne.
Mataimakin jakadan na Iran ya bayyana cewar ba karamin abin bakin ciki ba ne yadda ake ci gaba da kau da kai ba tare da hukunta Isra'ila kan irin take hakkokin al'ummar Palastinu da take yi ba ciki kuwa har da ci gaba da gina matsugunan yahudawa, rusa gidajen Palastinawa, kamawa da kuma ci gaba da tsare bugu da kari kan ci gaba da kai hare-hare wajaje masu tsarki da sahyoniyawa suke yi.
Daga karshe dai Mr. Dehqani ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da goyon bayan al'ummar Palastinu har sai sun tabbatar da 'yancinsu.