Ziyarar Ministan Tsaron Kasar Iran A Kasar Afirka Ta Kudu
Ministan tsaron kasar Iran ya kama hanya zuwa birnin Pretoria na kasar Afirka, domin fara gudanar da wata ziyarar aiki a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Irna ya bayar da rahoton cewa, ministan tsaron kasar ta Iran Janar Hussain Dehqan, ya bar birnin Tehran a yau, yakama hanya zuwa Afirka ta kudu, domin karba goron gayyatar da ya samu daga takwararsa ta kasar Afirka ta kudu Mapisa Nkakula.
Ziyar ta janar Dehqan dai za ta kwashe tsawon kwanaki biyu, inda zai gana da ministar tsaro ta Afirka ta kudu da ma wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin kasar, kamar yadda kuma za a rattaba hannu kan wasu muhimamn yarjeniyoyi na tsaro tsakanin Iran da Afirka ta kudu.
Kasar Afirka ta kudu dai na daya daga cikin kasashen nahiyar Afirka da suke da kyakyawar alaka da Iran, musamman a bangarori na tattalin arziki da cinikayya da kuma musayar ilimin kimiyya da fasaha a tsakanin kasashen kasashen biyu.