Ma'aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Jaddada Wajabcin Kalubalantar Ayyukan Ta'addanci
(last modified Wed, 25 Jan 2017 10:40:23 GMT )
Jan 25, 2017 10:40 UTC
  • Ma'aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Jaddada Wajabcin Kalubalantar Ayyukan Ta'addanci

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne a kan kasashen duniya su hada kai a fagen yaki da duk wani nau'in ayyukan ta'addanci.

A zaman hadin gwiwa tsakaninsa da shugaban rundunar 'yan sanda bangaren yaki da muggan kwayoyi a yau Laraba: Sayyid Abbas Arakche mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: babu wata kasa ita kadai da zata samu nasarar murkushe ayyukan ta'addanci a duniya, don haka dole ne sai an samu hadin kai da taimakekkeniya a tsakanin kasashen duniya.

Har ila yau Sayyid Arakche ya jaddada samun karin hadin gwiwa tsakanin kungiyoyin kasa da kasa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a fagen yaki da fataucin muggan kwayoyi musamman gani yadda kasar Iran take wahala a kokarin dakile fataucin muggan kwayoyin a kan iyakokin kasarta.