Ayatollah Khamenei: Amurka Ce Ummul-haba'isin Matsalolin Yankin Gabas Ta Tsakiya
Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana shigar shugular da Amurka ke yi a cikin harkokin kasashen yankin gabas ta tsakiya a matsayin ummul-haba'isin dukkanin matsalolin da suka addabi yankin.
Jagoran ya bayyana hakan ne a daren jiya a lokacin da yake ganawa da Firayi ministan kasar Sweden Stefan Lofan da yake gudanar da ziyarar aiki a Tehran.
Ayatollah Khamenei ya yi ishara da matsalolin baya-bayan nan da suke faruwa a yankin, musammana kasashen Syria da Iraki da kuma Yemen, inda ya ce Amurka tana amfani da hanyoyi na haddasa rikici a tsakanin al'ummomi domin cimma burinta na siyasa.
Dangane da batun yaki da ta'addanci kuwa, jagoran ya bayyana Amurka da wasu kasashe masu yi mata amshin shata a yankin a matsayin masu mara baya ga dukkanin ayyukan ta'addanci ad suka addabi gabas ta tsakiya.
A yayin da yake magana a kan jerin gwanon da al'ummar kasar Iran ta gudanar a ranar Juma'a da ta gabata kuwa a ranar da juyin juya halin muslunci ya cika shekaru 38 kuwa, jagoran ya bayyana hakan a matsayin wani martanin al'ummar kasar ga masu yi mata barazana.