Iran ce A gaba Wajen Fada Da Makaman Kare Dangi.
Ma'aikatar harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa; Iran ba za ta taba mancewa da hare-haren makamai masu guba da tsohon shugaban kasar Iraki, Sadam ya kawo wa al'ummar kasarta ba.
Ma'aikatar harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa; Iran ba za ta taba mancewa da hare-haren makamai masu guba da tsohon shugaban kasar Iraki, Sadam ya kawo wa al'ummar kasarta ba.
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Iraqche da ya ke jawabi a wurin kaddamar da wani littafi akan hare-haren makamai masu guba da Iraki ta kawo wa Iran, ya ce; Bayan wadancan hare-haren ne, duniya ta fahimci cewa wajibi ne a kawo karshen wadannan makamai da kuma hana adana su, balle kuma hana amfani da su.
Irakchi ya kara da cewa; Dubban mutanen da su ka yi shahada da kuma zama nakasassu sanadiyyar hare-haren na makamai mai guba, suna a matsayin wani sako ne mai kargi zuwa ga duniya akan zaluncin da aka yi wa al'ummar Iran.