Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Kirayi Jakadan Turkiya Da Ke Tehran
Ma'aiktar harkokin wajen Iran ta kirayi jakadan kasar Turkiya da ke Tehran, domin nuna masa rashin amincewa da kalaman da suka fito daga bakunan Erdogan da kuma ministan harkokin wajen Turkiya na batunci a kan Iran.
A lokacin da jami'an ma'aikatar harkokin wajen ta Iran suka gayyaci jakadan Turkiya a yau, sun bukaci da ya sanar da gwamnatin kasarsa cewa abin Erdogan da ministan harkokin wajensa suka fada na batunci a kan ya yi hannun riga da dukkanin ka'idoji na diflomasiyya, kuma Iran tana hakuri matuka, amma kuma hakurin yana da iyaka.
A ckin wannan makon ne Erdogan ya ziyarci wasu kasashen larabawan yankin tekun fasha, da suka hada da UAE, Saudiyyah da kuma Qatar, ya yi kalaman batunci a kan Iran, tare da bayyana ta a matsayin babban karfen kafa a gare su, musamman a kan siyasarsu a kasashen Syria da Iraki da kuma Yemen.
Shi ma a nasa bangaren ministan harkokin wajen Turkiya Jawish Auglo a lokacin da yake jawabi a gaban taron Munich na kasar Jamus da ake gudanarwa kan tsaro, ya maimaita abin da Erdogan ya fadi, wanda hakan ya yi daidai da abin da ministocin harkokin Saudiyya da na Isra'ila suka fada a kan Iran a wajen taron.