Ruhani: Matsalar Palastinu Wata Alama Ce Ta Gazawar Kungiyoyin Kasa Da Kasa
Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana cewar matsalar Palastinu ba matsala ce ta wata al'umma guda ba, face wata alama ce ta zalunci da take hakkoki wasu al'ummomi kana wani lamari da ke nuni da gazawar cibiyoyin kasa da kasa.
Shugaba Ruhani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabin rufe taro kasa da kasa na goyon bayan boren Intifadar al'ummar Palastinu da aka kawo karshensa a yau din nan a nan Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran inda yayin da yake ishara da irin zaluncin shekaru aru aru da sahyoniyawa suke yi wa al'ummar Palastinu da kuma gazawar da cibiyoyin kasa da kasa suka yi wajen kawo karshen hakan ya bayyana cewar lamarin Palastinun wata alama ce da ke nuni da gazawar da cibiyoyin kasa da kasa din suka yi.
A wani bangare na jawabin nasa, shugaba Ruhani ya jinjinawa al'ummar Palastinu wadanda suka mike wajen kwato hakkokinsu, kamar yadda yayi kakkausar suka da irin ayyukan ta'addancin da sahyoniyawan suke yi a kan al'ummar Palastinu yana mai kiran al'umma da su hada kansu waje guda don fuskantar wannan wuce gona da iri.
A shi ma a nasa bangaren, Alkalin alkalan Iran Ayatullah Sadeq Amoli Larijani, wanda ya gabatar da jawabinsa a safiyar yau ya inda ya ce babban kuskuren al'ummar musulmi su damfara fatansu da kuma jiran kasashen yammaci su taimaka musu wajen magance matsalolinsu musamman matsalar Palastinu, inda yace hanya guda ta magance matsalolin da ake fuskanta ita ce dogaro da Allah da kuma riko da tafarkin gwagwarmaya.
A jiya Talata ne dai aka bude taron kasa da kasa don goyon bayan Intifadar Palastinawa karo na 6 da ya sami halartar baki kimanin 700 daga kasashe 80 na duniya.