Feb 28, 2017 18:20 UTC
  • Sojojin Ruwan Iran Sun Gwada Wani Makami Mai Linzami Mai Tarwatsa Jiragen Ruwan Yaki

A rana ta karshe ta atisayen soji da suke yi, sojojin ruwa na kasar Iran sun sami nasarar gwada wani makami mai linzami da aka ba shi suna 'Wal Fajr" mai karfin tarwatsa jiragen ruwan yaki da masanan kasar suka kera cikin nasara.

Rahotanni daga fagen atisayen da aka ba shi sunan "Velayat 95" sun bayyana cewar a yau Talata ce dai sojojin ruwan na Iran suka gwada wannan makami mai linzamin daga daya daga cikin jiragen ruwan yakin da suke gudanar da atisayen inda ya tarwatsa wani jirgin ruwan da aka tsara shi a cikin ruwan.

Har ila yau kuma a yayin wannan atisayen da sojojin suka gudanar da shi yankuna daban-daban da suka hada da Mashigar Hormuz, Tekun Oman da kuma bangaren arewa na Tekun Indiya, sojojin sun gwada wasu dabarun yaki da kai hare-hare daga nesa kan wasu wajaje na makiya da aka tsara, kamar yadda kuma aka gwada wasu sabbin jiragen yaki masu saukar ungulu masu kai hare-hare kan jiragen ruwan yaki da kuma yadda suke ayyukansu.

Yayin da yake magana kan atisayen sojin, babban hafsan hafsoshin sojin ruwan na Iran Rear Admiral Habibollah Sayyari ya bayyana cewar manufar atisayen ita ce kara karfafa irin karfin da sojojin kasar Iran din suke da shi wajen kare kasar daga barazanar makiya.

 

Tags