Shugabannin Kasashen Iran Da Syria Sun Gudanar Da Tattaunawa
Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya tuntubi shugaba Bashar Assad na kasar Syria ta wayar tarho, dangane da harin da Amurka ta kaddamar a kan kasar Syria a Juma'ar da ta gabata.
A yayin tattaunawar, shugabannin kasashen Iran da Syria sun bayyana harin na Amurka a matsayin wani mataki na yin hawan kawara a kan dokoki na kasa da kasa.
Shugaba Rauhani ya ce, Amurka da kanta tare da hadin gwiwar majalisar dinkin duniya da wasu kasashe kamar Rasha da Iran da sauransu, suka yi aikin kwashe dukkanin sanadarai masu guba da ke kasar Syria, a kan haka zargin gwamnatin Syria da yin amfani da sanarai masu guba magana ce ta siyasa kawai, a kan haka ya zama wajibi a gudanar da bincike na gaskiya kan hakikanin abin da ya faru, maimakon cika duniya da farfaganda ta siyasa.
A nasa bangaren shugaba Assad na Syria ya mika godiyarsa ga shugaba Rauhani dangane da irin tsayin dakan da Iran ta yi wajen tunkarar manyan kasashen duniya masu girman kai da ke nufin rusa kasar ta Syria ta hanyar yin amfani da 'yan ta'addan takfiriyya.